Sojojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Hallaka Wasu 'Yan Kungiyar Boko Haram 21
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19558-sojojin_nijeriya_sun_sami_nasarar_hallaka_wasu_'yan_kungiyar_boko_haram_21
Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojinta sun sami nasarar hallaka wasu mayakan kungiyar Boko Haram su 21 da kuma ceto wasu mutane 1,623 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su bayan wani gumurzu a kauyen Jarawa na karamar hukumar Kale Balge da ke jihar Borno.
(last modified 2018-08-22T06:59:59+00:00 )
Apr 18, 2017 06:33 UTC
  • Sojojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Hallaka Wasu 'Yan Kungiyar Boko Haram 21

Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojinta sun sami nasarar hallaka wasu mayakan kungiyar Boko Haram su 21 da kuma ceto wasu mutane 1,623 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su bayan wani gumurzu a kauyen Jarawa na karamar hukumar Kale Balge da ke jihar Borno.

Daraktan yada labarai na rundunar sojin Nijeriyan Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce a yayin gumurzun da ya gudana tsakanin dakarun sojin da 'yan ta'addan na Boko Haram a kauyen na Jarawa, an hallaka 'yan Boko Haram 21 da kuma ceto wasu mutane 1623 da suke garkuwa da su wadanda ya ce a halin yanzu suna sansanin 'yan gudun hijira da ke Rann.

Har ila yau Janar Kukasheka ya ce dakarun na su sun sami nasarar kwace makamai da suka hada da bindigogi da gurneti-gurneti na hannu, da sauran nau'oi na makamai da kuma babura guda hudu.

Haka nan kuma kakakin sojin ya ce sojojin sun kakkabe ‘yan Boko Haram din daga  garuruwan Deima, Artano, Saduguma, Duve, Bardo, Kala, Bok, Msherde and Ahirde sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu.