Tattaunawa A Tsakanin Majalisar Dinkin Duniya Da Gwamnatin Kasar Congo.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19560-tattaunawa_a_tsakanin_majalisar_dinkin_duniya_da_gwamnatin_kasar_congo.
Majalisar dinkin duniya tana shiga tsakanin gwamnati da 'yan hamayyar kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:59+00:00 )
Apr 18, 2017 14:42 UTC
  • Tattaunawa A Tsakanin Majalisar Dinkin Duniya Da Gwamnatin Kasar Congo.

Majalisar dinkin duniya tana shiga tsakanin gwamnati da 'yan hamayyar kasar.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato cewa  "Maman Sidiko' wanda shi ne shugaban dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a  kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ya gana da shugaban jam'iyyar adawa ta (UDPS).

A bisa yarjejeniyar da aka cimmawa a ranar 31 ga watan Decemba na 2016, gwamnati da 'yan adawar Congo, za a nada dan adawa a matsayin pira minista na jiran kwarya. Sai dai shugaban kasar Joseph Kabila ya yi gaban kansa ya  nada Bruno Tshibala a matsayin pira ministan.

Jam'iyyun hamayyar kasar sun nuna kin aminewarsu da nadin pira ministan tare da bayyana shi da cewa ya sabawa yarjejeniyar da su ka kulla da gwamnati.

Har yanzu, jam'iyyun hamayyar siyasar kasar suna ci gaba da nuna kin yardarsu, abinda ya sa majalisar dinkin duniya ke shiga tsakanin domin warware rashin jituwar bangarorin biyu.