Tashin Bom Ya Jikkata Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19610-tashin_bom_ya_jikkata_dakarun_wanzar_da_zaman_lafiya_a_kasar_mali
Tashin wani bom a yankin arewacin Mali ya jikkata dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dikin Duniya da ke kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:59+00:00 )
Apr 19, 2017 13:17 UTC
  • Tashin Bom Ya Jikkata Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasar Mali

Tashin wani bom a yankin arewacin Mali ya jikkata dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dikin Duniya da ke kasar.

A wani bayani da majiyar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a yau Laraba yana dauke da cewa: Wani bom ya tashi a kan hanyar shigewar tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Mali a kan hanyarsu da ke garin Kidel a shiyar arewacin kasar lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatan dakarun wanzar da zaman lafiyan biyu tare da wani farar hula guda.

Wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar ta Mali Mahamed Saleh Annadif ya yi tofin Allah tsine kan wannan harin bom da ake zargin bisinewa aka yi, sannan ya bayyana tsananin bakin cikinsa kan yadda matakan tsaro suke ci gaba da tabarbarewa a yankunan da suke arewa da kuma tsakiyar kasar ta Mali.