Yan Gudun Hijirar Somaliya Fiye Da 61,000 Ne suka koma kasarsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19802-yan_gudun_hijirar_somaliya_fiye_da_61_000_ne_suka_koma_kasarsu
Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada labarin cewa: 'Yan gudun hijirar Somaliya fiye da 61,000 ne suka koma kasarsu daga kasar Kenya.
(last modified 2018-08-22T07:00:01+00:00 )
Apr 25, 2017 09:39 UTC
  • Yan Gudun Hijirar Somaliya Fiye Da 61,000 Ne suka koma kasarsu

Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada labarin cewa: 'Yan gudun hijirar Somaliya fiye da 61,000 ne suka koma kasarsu daga kasar Kenya.

Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Tun bayan fara jigilar 'yan gudun hijirar Somaliya zuwa kasarsu daga kasar Kenya a watan Disamban shekara ta 2014 zuwa yanzu, an samu nasarar komar da 'yan gudun hijira kimanin 61,665 zuwa kasarsu ta gado.

Sanarwar ta kara da cewa: A cikin kwanaki goma da suka gabata; 'yan gudun hijirar Somaliya kimanin 1,836 suka koma gida bayan shafe tsawon shekaru suna rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira da ke kasar Kenya.

Kididdaga tana nuni da cewa: 'Yan gudun hijirar Somaliya kimanin miliyan daya da dubu dari ne suke rayuwa a cikin kasar Kenya a matsayin 'yan gudun hijira, yayin da wasu kimanin 900,000 suke rayuwa a sauran kasashen da suke makobtaka da kasar ta Somaliya a matsayin 'yan gudun hijira.