Taron Masanan Kasashen Yammacin Afirka Kan Fada Da Ta'addanci A Kasar Togo
A ci gaba da kokarin samo hanyoyin da za a bi wajen fada da ta'addanci a kasashen Yammacin Afirka, masana harkokin tsaro daga kasashe 10 na Yammacin Afirka sun gudanar da wani taro a birnin Lome, babban birnin kasar Togo don tattauna hanyoyin da za a bi wajen fada da ta'addancin.
Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya bayyana cewar masana harkokin tsaro daga kasashen Togo, Benin, Burkina Faso, Ivory Coast, Guinea Bissau, Mali, Nijeriya, Nijar, Senegal da Cape Verde sun gudanar da wani taro na kwanaki biyu don tattauna hanyoyin tabbatar da tsaro a wadannan kasashen da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar ayyukan ta'addanci da ke faruwa a yankin.
Rahotannin sun ce daga cikin batutuwan da aka fi ba su muhimmanci a yayin wannan taron shi ne batun tsaron jiragen sama da suke yawo a yankin wadanda su ma suke fuskantar barazanar ta'addanci sakamakon irin raunin da ake da shi a bangaren ba su kariya.
Rahotannin sun ce baya ga masanan har ila yau kuma taron na kwanaki biyu ya sami halartar Nicolas Berlanga Martinez, jakadan kungiyar Tarayyar Turai a kasar Togon, Latta Dokisime Gnama, babban daraktan hukumar jiragen sama wadanda ba na soji ba na kasar Togon da kuma Bah-Traoré, babban jami'i mai shiga tsakani kungiyar tsaro na tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirkan (UEMOA).