An Tsawaita Doka Ta Maci Zuwa Wasu Watanni Shidda A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19940-an_tsawaita_doka_ta_maci_zuwa_wasu_watanni_shidda_a_kasar_mali
Majalisar dokokin kasar Mali ta amince da tsawaita doka ta baci a kasar har zuwa 31 ga watan Octoba mai zuwa, wato watammim shidda nan gaba.
(last modified 2018-08-22T07:00:02+00:00 )
Apr 30, 2017 09:24 UTC
  • An Tsawaita Doka Ta Maci Zuwa Wasu Watanni Shidda A Kasar Mali

Majalisar dokokin kasar Mali ta amince da tsawaita doka ta baci a kasar har zuwa 31 ga watan Octoba mai zuwa, wato watammim shidda nan gaba.

Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa gwamnatin Bamako ta fara kafa dokar ta baci ne tun ranar 20 ga watan Nuwamban shekara ta 2015 bayan wani mammunan hari wanda yan ta'adda suka kaiwa Radisson Blu Hotel wanda ya kai ga kashe mutane 20 daga ciki har da yanta'adda 2.

Da farko dai gwamnatin kasar ta Mali ta fara tsawaita dokar ta bacin ne a ranar 19 ga watan Afrilu shekara 2016 na tsawon kwanaki goma sannan bayan harin da yan tawaye suka kai kan birnin Timbuktu a rana 18 ga watan Afrilun shekara ta 2017 suka kashe mutane 5 sannan suka raunata wasu kimani 10 daga ciki har da sojojin kasar a lokacimma an kafa wata doka ta bacin .

 Har'ila yau a shekara ta 2015 gwamnatin kasar ta kulla yerjejeniya da sulhu tare da kungiyoyin yan ta'adda da dama daga arewacin kasar amma har yanzun an kasa aiwatar da shi.