Jami'an Gwamnatin Kasar Tunisia Da Dama Ne Suka Ajiye Ayyukansu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19944-jami'an_gwamnatin_kasar_tunisia_da_dama_ne_suka_ajiye_ayyukansu
Bayan tashe tashen hankula na wasu kwanaki a wasu yankunan kasar Tunisia daga karshe gwamnatin kasar ta sauya gwamnatin lardin Tadawin don dawo da zaman lafiya da nutsuwa a lardin.
(last modified 2018-08-22T11:30:02+00:00 )
Apr 30, 2017 13:56 UTC
  • Jami'an Gwamnatin Kasar Tunisia Da Dama Ne Suka Ajiye Ayyukansu

Bayan tashe tashen hankula na wasu kwanaki a wasu yankunan kasar Tunisia daga karshe gwamnatin kasar ta sauya gwamnatin lardin Tadawin don dawo da zaman lafiya da nutsuwa a lardin.

Tashar television ta Skynews ta bayyana cewa mutanen lardin Tadawin daga kuduncin kasar Tunisi sun yi ta gudanar da zanga zanga na tsawon makonni kimani uku don nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnan lardin take gudanar da harkokin tattalin arziki da zamantakewa na yankin na su.

Amma a jiya Asabar ne Priministan kasar Yusud Asshaheed ya dau matakin sauya gwamnan nada sabon gwamna a lardin na Tadawin don kwanatar da hankula. 

Banda haka a birnin Tunis babban birnin  kasar ma an yi ta gudanar da zanga zangar lumana don yin All..wadai da wani kudurin na aka gabatarwa majalisar dokokin kasar na yafewa barayin da suka sace kudaden gwamnatin a baya satar da suka yi tare da bukara su biya wasu harajin da za'a dora masu.