'Yan Sanda Sun Yi Awun Gaba Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido
'Yan sanda a Nijeriya sun yi awun gaba da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido saboda zargin kokarin tada da hankali da hana ruwa gudu yayin zaben kananan hukumomi da za a gudanar a jihar.
Kafar watsa labaran PREMIUM TIMES a Nijeriyan ta ce a yau Lahadi ne 'yan sandan suka kama tsohon gwamna Sule Lamidon a gidansa da Kano da kuma tafiya da shi zuwa helkwatar 'yan sandan da ke birnin na Kano inda suka tsare shi, sai dai an ce wasu na kurkusa da shi suna nan suna ta kai gwauro su kai mari wajen ganin an sako shi.
Rahotanni dai sun ce 'yan sandan suna zargin Alhaji Lamido ne da tunguza magoya bayansa a kokarin da yake yi na ganin ba a gudanar da zaben kananan hukumomi da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru ta shirya ba.
Baya ga wannan zargin har ila yau hukumar fada da zagon kasa ga tattalin arzikin kasar EFCC ma dai tana zargin tsohon gwamna Sule Lamidon da yin sama da fadi da wasu makudan kudaden jihar a lokacin yana mulkin lamarin da ya sanya aka taba daure shi a gidan yari tare da dansa saboda wannan zargin.