Fira Ministan Tunusiya Ya Tsige Ministar Kudin Kasar Daga Kan Mukaminta
Fira ministan Tunusiya ya sanar da tsige ministar kudin kasar Lamiya Zaribi daga kan mukaminta bayan kakkausar sukar da ta fuskanta daga bangaren 'yan adawar kasar sakamakon shirinta na tattalin arziki da ya janyo faduwar darajar kudin kasar.
Kakakin fira ministan Tunusiya a yammacin jiya Lahadi ya sanar da cewa: Fira ministan kasar Yusuf Sha'hid ya tube ministan kudin kasar Lamiya Zaribi daga kan mukaminta tare da maye gurbinta da Fadhil Abdul-Kafi ministan ma'aikatar kula da sanya hannayen jari ta kasar.
Tsige Lamiya Zaribi daga kan mukaminta na ministar kudin kasar ta Tunusiya ya zo ne bayan mako guda da babban bankin kasar ya fitar da sanarwar faduwar darajar kudin kasar dinar tare da hau hauwar darajar kudaden waje misalin dala da euro.
Lamiya Zaribi ta fara fuskantar kakkausar suka ce daga bangaren 'yan adawar Tunusiya tun bayan da ta gabatar da shawara kan hanyar da ta dace abi domin magance matsalar ci gaba da faduwar darajar kudin kasar amma sai shawarar nata ta kara janyo bullar matsalar ci gaba da faduwar darajar kudin kasar baya ga matsalar tafiyar hawainiya da harkar bunkasa tattalin arzikin kasar ta Tunusiya ke yi.