Ana Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Aljeriya
May 04, 2017 05:49 UTC
Yau Alhamis, 'yan Aljeriya kimanin miliyan 23 ke kada kuri'a a zaben 'yan malisar dokokin kasar.
'Yan takara 12,000 ke fafatawa a zaben domin samun gurbi a majalisar dokokin kasar mai kujeru 462.
An dai tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar inda aka zuba 'yan sanda 45,000 da zasu tabbatar da doka da oda a rufunan zaben.
Bayanai daga kasar sun nuna cewa yakin neman zaben bai yi armashi sosai ba.
Saidai sabuwar jam'iyyar tsohon firaministan kasar Ali Benflis ta kaucewa zaben.
Ali Benflis shi ne dai wanda ya sha kaye a zaben da aka fafata tsakanin shugaba mai ci Abdelaziz Bouteflika a zaben shugabancin kasar na 2014.
Tags