Dubban 'Yan Gudun Hijirar Somaliya Sun Koma Gida Daga Kasar Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20228-dubban_'yan_gudun_hijirar_somaliya_sun_koma_gida_daga_kasar_kenya
Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada labarin cewa: Dubban 'yan gudun hijirar Somaliya sun koma kasarsu daga kasar Kenya.
(last modified 2018-08-22T11:30:05+00:00 )
May 09, 2017 19:32 UTC
  • Dubban 'Yan Gudun Hijirar Somaliya Sun Koma Gida Daga Kasar Kenya

Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada labarin cewa: Dubban 'yan gudun hijirar Somaliya sun koma kasarsu daga kasar Kenya.

Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya {UNHCR} ta sanar da cewa: 'Yan gudun hijirar Somaliya da yawansu ya kai 23,058 ne da suke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijirar Dadaab da ke gabashin kasar Kenya suka koma kasarsu daga farkon wannan shekara ta 2017 da muke ciki.

Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijirar ta kuma fayyace cewa: A halin yanzu haka akwai jiragen sama da suke shirye su gudanar da jigilar 'yan gudun hijirar Somaliya da suke son komawa gida daga kasar Kenya zuwa lardin Kismayo na Somaliya da kuma birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa; Bullar matsalar cutar kwalara da na fari a kasar Somaliya a 'yan watannin baya-bayan nan suna daga cikin dalilan raguwar yawan 'yan gudun hijirar Somaliya da suke son komawa kasarsu ta gado daga kasar Kenya.