Mataimakin Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Ya Tsira Daga Harin Kisan Gilla
Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu ya tsallake rijiya da baya a wani harin kisan gilla da wasu 'yan bindiga suka kai kan ayarinsa a yau Talata.
Ministan watsa labaran kasar Sudan ta Kudu Jacob Akech Deng ya bayyana cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai harin wuce gona da iri kan ayarin mataimakin shugaban kasar Taban Deng Gai a yau Talata, inda suka jikkata uku daga cikin masu tsaron lafiyarsa amma mataimakin shugaban kasar bai samu koda rauni ba.
Ministan watsa labaran ya kara da cewa: 'Yan bindigan sun kai harin wuce gona da iri kan ayarin mataimakin shugaban kasar ne a kan hanyarsu ta zuwa garin Bor da ke gabashin kasar daga birnin Juba fadar mulkin kasar.
Tun a watan Disamban shekara ta 2013 kasar Sudan ta Kudu ta tsunduma cikin yakin basasa bayan da shugaban kasar Silva Kirr ya zargin mataimakinsa Riek Machar da hannu a shirya makarkashiyar kifar da gwamnatinsa lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwan dubban mutane tare da tilastawa wasu kimanin miliyan uku tserewa daga muhallinsu a matsayin 'yan gudun hijira.