Shugaban Hukumar Zaben Tunusiya Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20240-shugaban_hukumar_zaben_tunusiya_ya_yi_murabus
Shugaban hukumar zaben kasar Tunusiya, Chafik Sarsar, ya yi murabus da shi da wasu mukarabansa 12 na hukumar a wani al'amari da ya zo ma al'ummar kasar abun ba- zata.
(last modified 2018-08-22T11:30:05+00:00 )
May 10, 2017 05:50 UTC
  • Shugaban Hukumar Zaben Tunusiya Ya Yi Murabus

Shugaban hukumar zaben kasar Tunusiya, Chafik Sarsar, ya yi murabus da shi da wasu mukarabansa 12 na hukumar a wani al'amari da ya zo ma al'ummar kasar abun ba- zata.

Bayanai daga kasar sun ce shugaban hukumar da shi da mukarabansa 12 sunyi murabus ne saboda rashin gaskiya da kuma nuna son kai.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum dai na ganin cewa wannan matakin zai maida hannun agogo baya a shirye-shiryen zaben wakilan kananan hukumomin kasar, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan guguwar neman sauyin data yi awan gaba da mulkin shugaba Ben Ali a cikin shekara 2011.

A can baya dai, Chafik Sarsar da hukumar zaben kasar ta ISIE ta samu yabo da jinjina sosai akan rawar data taka a zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki a shekara 2014.

A ranar 17 ga watan Disamba na wannan shekara ne aka tsaida ranar gudanar da zaben, bayan shafe tsawan lokaci mai tsawo kafin kasar ta samu gindin zama bisa turbar demukuradiyya.