Jami'an Tsaron Aljeriya Sun Halaka Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Kasar
May 13, 2017 01:52 UTC
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da halaka wasu gungun 'yan ta'adda a lardin Ain-Defla da ke arewacin kasar.
A bayanin da ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta fitar a cikin daren jiya Juma'a ta fayyace cewa: Jami'an tsaron kasar sun kai wani samame a yankin Al-Ibadiyyah da ke lardin Ain-Defla a karkashin shirin yaki da ta'addanci a kasar, inda suka yi nasarar halaka wasu gungun 'yan ta'adda ta mutum biyar tare da gano wani rumbun makamai da na'urorin ayyukan leken asiri.
A cikin 'yan watannin baya-bayan nan jami'an tsaron Aljeriya sun tsananta gudanar da samame tare da kaddamar da hare-hare kan maboyar 'yan ta'adda musamman 'yan ta'addan kungiyar Al-Qa'ida a sassa daban daban na kasar.
Tags