Sudan Ta yi Furuci Da Mutuwar Sojojinta A Kasar Yemen.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20358-sudan_ta_yi_furuci_da_mutuwar_sojojinta_a_kasar_yemen.
Kakakin Sojan Kasar Sudan ya sanar a jiya asabar cewa an kashe sojojin kasar 2 a kasar Yemen.
(last modified 2018-08-22T11:30:06+00:00 )
May 14, 2017 06:35 UTC
  • Sudan Ta yi Furuci Da Mutuwar Sojojinta A Kasar Yemen.

Kakakin Sojan Kasar Sudan ya sanar a jiya asabar cewa an kashe sojojin kasar 2 a kasar Yemen.

Kakakin Sojan Kasar Sudan ya sanar a jiya asabar cewa an kashe sojojin kasar 2 a kasar Yemen.

Kamfanin Dillancin Labarun 'al-sharqul-Awsat" ya nakalto kakakin sojan kasar ta Sudan Ahmad Khalifah al-shami yana tabbatar da mutuwar sojojin biyu tare da jikkatar da wasu masu yawa kasar ta Yemen.

Kakakin sojojin kasar ta Sudan bai ambaci ko a wane yankin na kasar Yemen ne aka kashe sojojin kasar tasu ba.

Tun a cikin watan janairu na 2016 ne kasar Sudan ta sanar da kashe sojojinta na farko a  yankin Aden na  kasar Yemen, inda su ke taya kasar Saudiyya yaki da al'ummar kasar Yemen.

Taron dangin da larabawa su ka yi wa kasar Yemen wacce ita ce kasar larabawa mafi talaunci a tsakaninsu, ya ci rayukan mutane 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya. Miliyoyin mutanen kuma sun zama 'yan gudun hijira a cikin kasarsu, kamar kuma yadda yaki ya lalata muhimman cibiyoyin kasar da su ka hada da asibitoci.