Kotu Na Duba Yiyuwar Ba Da Damar Kada Kuri’ar Tsige Shugaba Zuma
(last modified Wed, 17 May 2017 05:52:37 GMT )
May 17, 2017 05:52 UTC
  • Kotu Na Duba Yiyuwar Ba Da Damar Kada Kuri’ar Tsige Shugaba Zuma

Babbar kotun kasar Afirka Ta Kudu na dubi dangane da ko za ta ba wa ‘yan majalisar kasar damar kada kuri’ar rashin amincewa da mulkin shugaban kasar Jacob Zuma a boye a daidai lokacin da wasu daruruwan mutane suke ci gaba da zanga-zangar kin jininsa a birnin Johannesburg.

Rahotanni daga kasar sun bayyana cewar ‘yan adawan kasar ne suka bukaci da a kada kuri’ar a asirce saboda da dama daga cikin ‘yan majalisar da ke wakiltar jam’iyyar ANC mai mulki a kasar suna fuskantar matsin lambar sai dai su kada kuri’ar amincewa da shugaba Zuman ya ci gaba da mulki. Don haka suka ce ya zama wajibi a gudanar da kuri’ar a asirce don hakan zai ba su kariya.

Shugaban majalisar dai Baleka Mbete, ya ki amincewa da bukatar ‘yan adawan na kada kuri’ar a asirce yana mai cewa ba shi da karfin yin hakan.

Hakan ne ya sanya ‘yan adawar bukatar babban kotun tsarin mulki ta kasar ba da umurnin kada kuri’ar a asirce wanda ‘yan adawan suke ganin zai ba da damar tsige shugaba Zuman da ke ci gaba da fuskantar matsin lambar sai ya sauka daga mulkin kasar.