Gwamnatin Tunusiya Ta Kara Wa'adin Dokar Ta Baci A Kasar
May 17, 2017 11:59 UTC
Shugaban kasar Tunusiya ya kara wa'adin dokar ta baci a kasar na tsawon wata guda.
Bayan gudanar da zaman tattaunawa da Majalisar ministocin Tunusiya da Majalisar Dokokin Kasar a jiya Talata: Shugaban kasar ta Tunusiya Qa'id Al-Sibsi ya sanar da karin wa'adin dokar da baci na tsawon wata guda a duk fadin kasar.
Tun bayan harin ta'addanci da aka kai kan motar bus da ke dauke da dakarun tsaron fadar shugaban kasar Tunusiya a ranar 24 ga watan Nuwamban shekara ta 2015 da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro fiye da 40, kuma kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta dauki alhakin kai harin, aka kafa dokar ta baci a duk fadin kasar, kuma ake kara wa'adinsa lokaci zuwa lokaci.
Tags