Kenya: An Kame 'Yan Kungiyar al-Shabab Akan Iyaka Da Somaliya
"yansandan kasar Kenya sun sanar da kame 'yan kungiyar al-shabab da dama akan iyaka rsu da kasar Kenya.
"yan sandan kasar Kenya sun sanar da kame 'yan kungiyar al-shabab da dama akan iyaka rsu da kasar Kenya.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato Micheal Kioni jami'in 'yan sandan garin Lamu da ke kan iyaka yana cewa; Daga watan Decemba na shekarar da ta gabata zuwa watan Maris, na wannan shekarar ta 2017, sun kame yan kungiyar ta al-shabab 33.
Jami'in yan sandan ya jaddada cewa; 'yan kungiyar ta al-shabab sun zo ne da zummar kai hare-haren ta'addanci a cikin yankunan arewa maso gabacin kasar.
A sshekarar da ta gabata ma dai jamian tsaron kasar ta Kenya ya sanar da kame wasu 'yan kungiyar ta al-shabab su 36.
Kungiyar al-shabab ta Somaliya tana a matsayin barazana ta tsaro ga kasashen makwabta da su ka hada da Kenya.