MDD: Dole Ne A Kai Agajin Gaggawa A Yankin Tafkin Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20582-mdd_dole_ne_a_kai_agajin_gaggawa_a_yankin_tafkin_chadi
Majalisar dinkin duniya ta ce ya zama wajibi a kai daukin gaggawa a yankin tafkin Chadi, domin kubutar da dubban mutane da suka shiga cikin halin lahaula.
(last modified 2018-08-22T07:00:08+00:00 )
May 21, 2017 12:47 UTC
  • MDD: Dole Ne A Kai Agajin Gaggawa A Yankin Tafkin Chadi

Majalisar dinkin duniya ta ce ya zama wajibi a kai daukin gaggawa a yankin tafkin Chadi, domin kubutar da dubban mutane da suka shiga cikin halin lahaula.

Shafin yada labarai na Afirka Time ya bayar da rahoton cewa, babban jami'in majalisar dinkin dinkin duniya a kan harkokin agajin gaggawa  Stephen O'Brien ya bayyana cewa, bisa la'akari da mawuyacin halin da wasu dubban fararen hula suke ciki a yankin tafkin Chadi, sun ware kudi kimanin dalar Amurka miliyan 3.5, domin kai daukin gaggawa gare su.

Ya ce a halin yanzu sakamakon matsalolin tsaro da suka gurgunta dukkanin harkokin rayuwa  ayankin, akwai mutane kimanin dubu 40 da suke butar daukin gaggawa, musamman ta fuskar abinci da tsaftataccen ruwan rasha, da suka hada da mata da kananan yara, wadanda ya ce nan da 'yan kwanaki masu zuwa taimakon zai isa zuwa gare su.