Shugabannin Kasashen Uganda Da Tanzaniya Sun Bukaci Dage Takunkumi Kan Kasar Burundi
(last modified Mon, 22 May 2017 06:18:05 GMT )
May 22, 2017 06:18 UTC
  • Shugabannin Kasashen Uganda Da Tanzaniya Sun Bukaci Dage Takunkumi Kan Kasar Burundi

Shugabannin kasashen Uganda da Tanzaniya sun bukaci dage takunkumin da kungiyar tarayyar Turai ta kakaba kan kasar Burundi.

Shafin Afrika Time ya habarta cewa: A ganwar da ta gudana tsakanin shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli da takwararsa na Uganda Yoweri Museveni a birnin Daru-Salam na Tanzaniya: Shugabannin biyu sun jaddada bukatar dage takunkumin da kungiyar tarayyar Turai ta kakaba kan gwamnatin Burundi.

A gefe guda kuma wannan bukata ta shugabannin Uganda da Tanzaniya ta fuskanci maida martani daga jakadar kungiyar tarayyar Turai a kasar Tanzaniya Roeland Van de Geer, inda ya jaddada bukatar ci gaba da aiwatar da takunkumi kan gwamnatin Burundi saboda kasancewarta ummul-haba'isin bullar tashe-tashen hankula a kasar ta Burundi.

Rikicin siyasa ya kunno kai ne a kasar Burundi tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya dauki matakin yin tazarce a kan karagar shugabancin kasar a wa'adi na uku lamarin da ya yi hannun riga da kundin tsarin mulkin kasar da ya gindaya sharadin yin wa'adi biyu kacal a kan karagar shugabancin kasar.