MDD Ta Yi Allah Wadai Da Kashe Sojojinta Biyu A Mali
May 24, 2017 06:38 UTC
Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai kan harin da aka kai ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Mali.
Kwamitin ya kuma nuna damuwarsa matuka kan yanayin tsaron kasar ta Mali, inda ya nemi bangarorin kasar da abin ya shafa da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba.
Dakarun MDD biyu ne dai suka mutu yayin da daya ya jikkta a harin kwantan bauna da aka kai masu a kusa da yankin Aguelhok dake arewa maso gabashin kasar ta Mali.
Tun dai fara aikinta a watan Yuli na shekara 2013 tawagar MINISMA ta rasa dakarunta dake aikin tabbatar da zamen lafiya a Mali guda 70.
Tags