IS Ta Dauki Alhakin Kai Harinta Na Farko A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20672-is_ta_dauki_alhakin_kai_harinta_na_farko_a_somaliya
Kungiyar ýan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar a yankin Bossasso dake arewacin kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T07:00:09+00:00 )
May 24, 2017 06:39 UTC
  • IS Ta Dauki Alhakin Kai Harinta Na Farko A Somaliya

Kungiyar ýan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar a yankin Bossasso dake arewacin kasar Somaliya

Wannan dai shi ne hari na farko da kungiyar ta dauki alhakin kaiwa a wannan kasa ta Somaliya.

A sanarwar data wallafa a shaffinta na Amaq kungiyar ta ce mutiminta ne ya kai harin da irin rigar  boma-bomai.

A jiya Talata ne dan kunar bakin waken ya tarwatsa kansa a daidai lokacin da jamián tsaro suka tsare shi a daidai wajen wani shinggen bincike.