Shugaban Kasar Aljeriya Ya Nada Sabon Fira Minista A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20686-shugaban_kasar_aljeriya_ya_nada_sabon_fira_minista_a_kasar
Shugaban kasar Aljeriya ya nada tsohon ministan gidaje na kasar a matsayin sabon fira ministan Aljeriya a wani garambawul da ya gudanar a gwamnatin kasar a yau Laraba.
(last modified 2018-08-22T11:30:09+00:00 )
May 24, 2017 18:52 UTC
  • Shugaban Kasar Aljeriya Ya Nada Sabon Fira Minista A Kasar

Shugaban kasar Aljeriya ya nada tsohon ministan gidaje na kasar a matsayin sabon fira ministan Aljeriya a wani garambawul da ya gudanar a gwamnatin kasar a yau Laraba.

Fadar shugaban kasar Aljeriya ta fitar da wata sanarwa a yau Laraba cewa: Shugaban kasar Abdul-Aziz Boutafliqa ya nada tsohon ministan gida na kasar Abdulmajid Tebboune a matsayin sabon fira minista da ya maye gurbin Abdelmalek Sellal a wani garambawul da ya gudanar a gwamnatin kasar.

A karkashin ayar doka ta 91 a kundin tsarin mulkin kasar Aljeriya shugaban kasa yana da hurumin daukan matakin canja fira minista, don haka a bayan gudanar da zaman tattaunawa da Majalisar Dokokin kasar; Shugaba Abdul-Aziz Boutafliqa ya sanar da Abdulmajid Tebboune a matsayin sabon fira ministan kasar.

Rahotonni suna bayyana cewa: Akwai yiyuwar a jinkirta kafa sabuwar majalisar ministocin Aljeriya zuwa bayan gudanar da zabukan 'yan Majalisun Dokokin kasar a wata mai kamawa na Yuni.