Kungiyar Kare Hakin Bil-adama ta zarkin Gwamnatin Ugnada Da Kasawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20758-kungiyar_kare_hakin_bil_adama_ta_zarkin_gwamnatin_ugnada_da_kasawa
Kungiyar kare hakin bil-adama ta Afirka ta zarkin Gwamnatin Uganda da kasawa wajen bayar da tsaron da ya dace ga fararen hula
(last modified 2018-08-22T11:30:10+00:00 )
May 27, 2017 06:21 UTC
  • Kungiyar Kare Hakin Bil-adama ta zarkin Gwamnatin Ugnada Da Kasawa

Kungiyar kare hakin bil-adama ta Afirka ta zarkin Gwamnatin Uganda da kasawa wajen bayar da tsaron da ya dace ga fararen hula

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Maria Burnett Daraktar Ofishin Kungiyar Kare hakin bil-adama na Afirka a jiya juma'a na cewa harin da aka garin Kasese na yammacin kasar Uganda a ranikun 26 da kuma 27 na watan Nuwambar 2016 yayi sanadiyar mutuwar sama da 150, kuma hasarar rayukan da aka yi shi ne irinsa na farko tun bayan da kasar Uganda ta fara fada da 'yan tawaye.

Jami'ar ta zarki Gwamnatin kasar Uganda da rashin niya da ta dace wajen gudanar da bincike dangane da yadda abin ya auku.

A watan Nuwambar 2016 ne Dakarun hadin gwiwar Sojoji da 'yan sanda suka kai hari fadar wani basaragen galgajiya a garin Kasese tare da kashe mutane sama da 155.