Jiragen Yakin Masar Sun Kai Hari Sansanin 'Yan Ta'adda A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20764-jiragen_yakin_masar_sun_kai_hari_sansanin_'yan_ta'adda_a_libiya
Bayan Harin da wasu 'yan ta'adda suka kaiwa mabiya addinin Kirista a jihar Minya na kasar Masar, Sojojin saman kasar Sun yi lugudar wuta kan wuraren 'yan ta'adda a Libiya.
(last modified 2018-08-22T07:00:10+00:00 )
May 27, 2017 01:56 UTC
  • Jiragen Yakin Masar Sun Kai Hari  Sansanin 'Yan Ta'adda A Libiya

Bayan Harin da wasu 'yan ta'adda suka kaiwa mabiya addinin Kirista a jihar Minya na kasar Masar, Sojojin saman kasar Sun yi lugudar wuta kan wuraren 'yan ta'adda a Libiya.

Tashar Telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Rundunar tsaron Masar cikin wani bayyani da fitar ta ce: Jiragen yakin kasar sun kai hari har so 6 a sansanin koyar da aiyuka Soja na 'yan ta'adda a garin Derna na gabashin kasar Libiya.

Rundunar ta ce ta kai harin ne bayan da ta tabbatar da cewa 'yan ta'addar dake wannan sansani na da hannu a harin daka kai wa mabiya addinin kirista jiya a kasar ta Masar.

A nasu bangaren Dakarun tsaron kasar Libiya dake goyon bayan Janar Khalifa Haftar sun tabbatar da cewa sun halarci hare-haren da aka kaiwa sansanin 'yan ta'addar na garin Derna, sannan kuma sun ce 'yan ta'addar nada alakar kut da kut da kungiyar ta'addancin nan ta Alka'ida kuma Sojojin kasar za ci gaba da kai musu farmaki ta kasa.

A daren jiya Juma'a, Shugaban kasar Masar Abdulfatah Alsese ya sanar da kai wannan hari, sannan kuma ya ce babu gudu babu ja da baya za su ci gaba da kai hare-hare a maboyar 'yan ta'adda a ciki da wajen kasar, bayan ga haka ya bukaci a hukunta dukkanin kasashen dake goyon bayan 'yan ta'adda.

A jiya Juma'a ce wasu Mahara guda goma suka kai hari kan wasu Bas Bas guda biyu dake dauke da mabiya addinin Kirista a jihar Minya na kasar Masar, inda suka kashe 28 tare da jikkata wasu 24 na daban daga cikin su.