An Kammala Zaben Sabon Shugaban Kasar A Kasar Benin A Jiya Lahadi
An gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Benin a jiya Lahadi inda masu zabe a kasar zasu zabi mutum guda a cikin yan
An gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Benin a jiya Lahadi inda masu zabe a kasar zasu zabi mutum guda a cikin yan takara 33 wanda zai gaji shugaba Thomas Bony Yayi a kan kujerar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto kafafin yada labarai na kasar sun bayyana cewa mutane miliyon 4.6 ne suka cancanci kada kuri'unsu a zaben na jiya kuma jam'iyyar mai mulki ta Boni yayi ta tsaida Priministan kasar Lionel Zinsou a matsayin dan takaranta. Kuma jam'iyyar adawa mafi girma a kasar dai ita ce Democratic Renewal Party.
Shugaban Bony Yayi dai zai sauka kan kujerar shugabancin kasar bayan da kundin tsarin mulkin kasar ya hana shi tsayawa karo na ukku. Yayi ya sabawa shuwagabannin Afrika da dama wadanda suke son yin ta zarce kan kujerun shugabancin kasashensu bayan cikar wa'adinsu.