Hukumar Zaben Kasar Kenya Ta Sanar Da Sunayen 'Yan Takarar Shugabancin Kasar
(last modified Tue, 30 May 2017 06:58:01 GMT )
May 30, 2017 06:58 UTC
  • Hukumar Zaben Kasar Kenya Ta Sanar Da Sunayen 'Yan Takarar Shugabancin Kasar

Hukumar zaben kasar Kenya ta sanar da sunayen mutane takwas da suka cancanci tsayawa takarar shugabancin kasar.

Hukumar zaben kasar Kenya a jiya Litinin ta fitar da sunayen mutane takwas da suka cancanci tsayawa takarar shugabancin kasar bayan gudanar da tankade da rairaya a sunayen masu son tsayawa takarar, kuma cikin mutanen da suka tsallake tantancewar har da shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyata da madugun 'yan adawar kasar Reila Ordingan.

Sauran mutanen da suka samu nasarar tsallake tankade da rairayar sun hada da 'yan takara uku da basu da wata jam'iyya wato 'yan indafenda, sannan sauran 'yan takarar uku da suka fito daga kananan jam'iyyun kasar.

A karkashin kundin tsarin mulkin kasar Kenya dai, dole ne dan takarar shugabancin kasar ya zame haifaffen kasar Kenya, kuma yayi karatunsa ne a daya daga cikin jami'o'in kasar, sannan dole ne yayi murabus daga kan duk wani matsayi da yake rike da shi a karkashin gwamnatin kasar. Za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Kenya ne a ranar 8 ga watan Agustan wannan shekara da muke ciki ta 2017.