Chadi : An Kori Ministoci biyu Saboda Almubazzaranci
(last modified Wed, 31 May 2017 05:52:33 GMT )
May 31, 2017 05:52 UTC
  • Chadi : An Kori Ministoci biyu Saboda Almubazzaranci

Shugaba Idriss Deby Itmo na Chadi ya kori wasu ministocinsa biyu bisa zargin almubazzaranci da dukiyar kasa.

Wata sanarwa da aka karanto a gidan radiyo na kasar ta ce shugaba Deby ya sanya hannu kan wani kudiri na korar ministocin biyu da suka hada dana tsare-tsare Hamid Mahamat Dahalob, da kuma na ma'adinai David Houdeingar, saidai ba tare da yin karin haske ba.

Amman wata majiya a kusa da gwamnatin kasar da bata so a ambaci sunnanta ba ta shaidawa kamfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa wani kwamitin bincike na gwamnatin kasar ya bankado  sunayen ministocin biyu cikin wata haraka ta almubazzaranci da dukiyar kasa.

David Houndeingar wanda ya kasance tsohon sakatare janar a fadar shugaban kasar, yayin da shi kuwa Hamid Mahamat Dahalob ya taba rike mukamin ministan shari'a.

Kasar Chadi dai wacce aminiyar Faransa ce a yaki da ta'addanci a yankin Sahel na fuskanci babban kalubale na tabarbarewar tattalin aziki  sabowa faduwar farashin mai.