An Kai Harin Ta'addanci A Wani Shingen Bincike A Kasar Algeria
(last modified Thu, 01 Jun 2017 11:53:02 GMT )
Jun 01, 2017 11:53 UTC
  • An Kai Harin Ta'addanci A Wani Shingen Bincike A Kasar Algeria

Wasu yan ta'adda sun kai hari a wani wuri bincike a kudancin birnin Algies babban birnin kasar Algeria

Jaridar "النهار" ta kasar Algeria ta nakalto majiyar jami'an tsaron kasar tana bayyana cewa a jiya Laraba wasu yan ta'adda sun bude wuta kan jami'an jandarmari a wani wurin bincike a yankin "واد جمعه" a cikin Lardin Baleeda kilomita 50 daga kudancin birnin Algies babban birnin kasar. 

Labarin ya kara da cewa jami'an tsaro na Jandarmari guda biyu ne suka ji raunuka masu tsanani a wannan harin. amma dayansu ya rasu daga baya a asbiti sanadiyyar raunukan da ya samu.

A halin yanzu dai hadin guiwan jami'a tsaron kasar na sojoji da jandar marsi sun fara bincke don gano yan ta'addan da suke da hannu harin na jiya.