An Kai Harin Ta'addanci A Wani Shingen Bincike A Kasar Algeria
Wasu yan ta'adda sun kai hari a wani wuri bincike a kudancin birnin Algies babban birnin kasar Algeria
Jaridar "النهار" ta kasar Algeria ta nakalto majiyar jami'an tsaron kasar tana bayyana cewa a jiya Laraba wasu yan ta'adda sun bude wuta kan jami'an jandarmari a wani wurin bincike a yankin "واد جمعه" a cikin Lardin Baleeda kilomita 50 daga kudancin birnin Algies babban birnin kasar.
Labarin ya kara da cewa jami'an tsaro na Jandarmari guda biyu ne suka ji raunuka masu tsanani a wannan harin. amma dayansu ya rasu daga baya a asbiti sanadiyyar raunukan da ya samu.
A halin yanzu dai hadin guiwan jami'a tsaron kasar na sojoji da jandar marsi sun fara bincke don gano yan ta'addan da suke da hannu harin na jiya.