An Kori Shugaban 'Yan Sandar Kasar Afirka Ta Kudu.
(last modified Fri, 02 Jun 2017 06:33:10 GMT )
Jun 02, 2017 06:33 UTC
  • An Kori Shugaban 'Yan Sandar Kasar Afirka Ta Kudu.

A Dakatar Da Shugaban 'Yan Sandar Afirka ta Kudu bayan da same shi da lafin barnar dukiyar kasa

Kamfanin dillancin labaran hukumar Telbijin da Radio na Iran ya nakalto Fikile Mbalula Ministan Ma'aikatar 'yan sanda ta kasar Afirka ta kudu a jiya Alkhamis na cewa bincike ya samu Khomotso Phahlane Shugaban Hukumar 'yan sandar kasar da hannu dumu-dumu wajen barnar dukiyar kasa, domin haka bai caccanci ci gaba da zama a kan mikaminsa ba.

Sanarwar ta sanar da sunan Letseja Mothiba a matsayin wanda ya maye gurbin Khomotso Phahlane.

Kafin hakan dai sabon Shuganan 'yan Sandar ta kasar Afirka ta Kudu Letseja Mothiba ya kasance Shugaban 'yan sanda na Jihar Gauteng dake arewa maso gabashin kasar Afirka ta Kudun.