Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Musanta Mallakar Gida A Dubai
(last modified Sun, 04 Jun 2017 18:04:03 GMT )
Jun 04, 2017 18:04 UTC
  • Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Musanta Mallakar Gida A Dubai

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya musanta jita-jita da zargin da ake masa cewa ya mallaki wani makeken gida a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wanda wasu 'yan kasuwa suka saya masa.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar, shugaba Zuman ya musanta wannan zargin ne  cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a yau din nan Lahadi inda ya ce: Shugaba Zuma ba shi da wata kadara a wajen kasar Afirka ta Kudu, sannan kuma bai bukaci wani ya saya masa wata kadara a waje ba. Don haka labarin wannan gida na Dubai karya ce kawai.

Jaridar Sunday Times ta Afirka ta Kudun ne ta buga labarin cewa wasu majiyoyi masu yawa sun tabbatar mata da cewa Iyalan Gupta, wadanda wasu gungun attajiran kasar Indiya, su ne suka saya wa Mr. Zuma wannan gidan a birnin na Dubai da aka ce ya kai Dala miliyan 25; lamarin da Iyalan Gupta din suka musanta.

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai ana zargin shugaban kasar Afirka ta Kudun da batun rashawa da cin hanci da kuma amfani da kudaden gwamnati wajen gyara gidansa na kansa da sauran zarge-zarge lamarin da ya sanya 'yan adawa suke ci gaba da kiran da ya sauka daga karagar mulki.