D.R Congo : An Fara Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Kisan Jami'an MDD
Wata kotun soji a Jamhuriya demukuraddiyar Kongo ta fara zamen shari'a wasu mutane da ake zargi da kashe jami'an MDD na biyu a yankin Kassai.
A jiya ne dai aka gurfanar da mutanen gaban kotun barikin sojin Kananga, saidai kuma an daga shari'ar har zuwa ranar 12 ga watan nan bisa bukatar ma'aikatar al'umma ta kasar.
Mutanen nan biyu dai da suka da hada dan shekaru 16 da kuma wani mai shekaru 30 ana zarginsu da laifin yaki tan hanyar kisa da kuma ta'addanci da kuma tada zaune tsaye.
Saidai lauyen dake kare mutanen ya yi watsi da duk zarge-zagren.
A watan Mayu da ya gabata mutane 16 ne aka tsare bisa zargin kisan jami'an MDDn da suka hada da Michael Sharp da Zaida Catalan wadanda ke cikin wani gungun kwararu dake bincike kan wasu mayan kaburbura da aka gano a yankin.