Bakin Haure Yan Kasar Senegal Sun Koma Gida Daga Kasar Libya
Daruruwan bakin haure wadanda suke mafarkin zuwa kasashen Turai daga kasar Senegal sun koma gida bayan sun sha zaman kaso a kasar Libya
Kamfanin dillancin Labaran reuters ya bayyana cewa daruruwan yan kasar Senegal wadanda aka tsare a gidajen kaso a kasar Libya na wani lokaci daga karshe an maidasu gida Senegal a cikin makonni da suka gabata.
Tawaga ta karshe na matasa yan kasa da shekaru 30, 160 da suka sauka a tashar jiragen sama na birnin Daka a jiya talata an mika su ga jami'an shige da fishe na kasar don tabbatar da cewa su yan kasar ta senegal ne.
The International Organization for Migration (IOM) da kuma gwamnatin kasar ta Senegal ne suka hada kai wajen maida yan kasar ta Senegal zuwa gida daga gidajen kurkukun da suke zama a kasar ta Libya.
Akalla bakin haure kimani dubu 20 ne suke tsare a gidajen yari daban daban na kasar Libya wadanda suka kasa tsallakawa zuwa kasashen turai.