MDD Ta Yi Tir Da Kashe Jami'anta Uku A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21188-mdd_ta_yi_tir_da_kashe_jami'anta_uku_a_mali
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da aka kai kan jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD a Mali, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar jami'ai uku.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 10, 2017 01:21 UTC
  • MDD Ta Yi Tir Da Kashe Jami'anta Uku A Mali

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da aka kai kan jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD a Mali, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar jami'ai uku.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a jiya Juma'a, Sakatare Janar din ya ce harin da aka kai wa jami'an a birnin Kidal ka iya zama laifin yaki. 

Antonio Guterres ya kuma jadadda goyon bayan MDD wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta yankin yammacin Afrika, yana mai jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun lafiya cikin gaggawa.

A cewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA, an farwa sansaninta da makaman roka a birnin Kidal a ranar Alhamis da ta gabata. 

Jami'an MDD uku ne 'yan asalin kasar Guinea suka rasa rayukansu, a harin da wani reshen kungiyar Al'Qaida ya dauki alhakin kaiwa.

Jim kadan bayan nan ne kuma, aka farwa jami'ai dake wajen sansanin, al'amarin da ya yi sanadin raunatar 8 daga cikinsu.