Dakarun Somaliya Sun Ragargaza Wani Sansanin Al-Shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21242-dakarun_somaliya_sun_ragargaza_wani_sansanin_al_shabab
Dakarun musamen na Somaliya hadin gwiwa da wani harin jiragen sama na Amurka ya kai mummunan hari kan wani sansanin bada horo na kungiyar Al-Shabaab a kudu maso yammacin Mogadisho babban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 12, 2017 01:13 UTC
  • Dakarun Somaliya Sun Ragargaza Wani Sansanin Al-Shabab

Dakarun musamen na Somaliya hadin gwiwa da wani harin jiragen sama na Amurka ya kai mummunan hari kan wani sansanin bada horo na kungiyar Al-Shabaab a kudu maso yammacin Mogadisho babban birnin kasar.

Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed ne ya bada umurnin kai harin, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta sanar.

Sanarwar ta ce bayan harin da aka kaddamar an yi nasarar lalata babbar tungar mayakan na Al-Shabaab dake kusa da Sakow, a tsakiyar yankin Jubba, wannan kuma a cewarsa zai rage barazanar hare-haren mayakan na Al-Shabaab.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da kungiyar ta Al'shabab ta ce ta kai wani mumunan hari kan sansanin sojin Somaliya a yankin Putland, inda ta ce ta kashe dakaru 61.