Senegal Ta jaddada Wajabcin Fada Da Ayyukan Ta'addanci
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya fadi cewa kasarsa za ta ci gaba da yaki da ta'addanci har zuwa dawowar tsaro.
Shugaba Macky Sall wanda ya gana da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana fatansa na ganin cewa; Sauran kasashe da su ke aiki tare da Senegal, musamman ma dai kasashen mambobi na kungiyar tattalin arziki na yammacin Afirka, za su ci gaba da aiki tare har zuwa dawowar zaman lafiya.
Shugaban na kasar Senegal ya kuma kara da cewa; Hadin kan da kasashen yankin su ke da shi tare da kasar Senegal zai zama mai kalubalantar masu wuce gona da iri da su ka jefa tsaron yankin cikin hatsari.
A nashi gefen, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya jinjinawa kasar ta Senegal ne saboda rawar da ta ke takawa a yaki da ta'addancin da ake yi a yankin.
Kasashen yankin na Afirka suna fuskantar matsalolin ta'addanci da kuma talauci da rikice-rikice na cikin gida.