Matsin Lamabar Saudiya Ga Kasar Somaliya
Majiyoyin Kasar Somaliya sun sanar da cewa Saudiya ta yi alkawarin bawa kasar Somaliya Dalar Amurka miliyan 80 domin ta goyi bayansa tare kuma da yanke alakar ta da kasar Qatar
A cikin wani rahoto da ta fitar a wannan Talata, Jaridar Somal-Alyaum ta habarta cewa magabatan Saudiya sun yi barazanar watsi da alkawarin da suke yi na taimakawa kasar da kudi, matukar dai ba ta canza siyasar ta ba ta ba ruwan mu dangane da rikicin da wasu kasashen Larabawa suke yi da kasar Qatar.
Rahoton ya ce ya zuwa yanzu magabatan kasar Somaliyan sun ki amincewa da shawarar da Saudiya ta gabatar musu.
A ranar Litinin 5 ga watan Yunin, wasu kasashen Larabawan Tekun Fasha da suka hada da Saudiya, hadaddiyar daular Larabawa, Libiya, Bahrein, da Masar suka yanke alakar su da kasar Qatar bisa zarkin cewa tana taimakawa aiyukan ta'addanci, zargin da magabatan kasar suka musanta,
Wannan rikici dai ya taso ne kwanaki bayan ziyarar Shugaba Trump na Amurka zuwa birnin Riyad na Saudiya, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin cewa shi ne ya haddasa shi.