Damuwar MDD Kan Ci Gaba Da Rikicin Siyasa A Tsakiyar Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21306-damuwar_mdd_kan_ci_gaba_da_rikicin_siyasa_a_tsakiyar_afirka
Manzon Musaman Na MDD zuwa kasashen dake tsakiyar Afirka ya bayyana damuwar sa kan ci gaba da rikicin Siyasa a yankin.
(last modified 2018-08-22T07:00:15+00:00 )
Jun 14, 2017 07:24 UTC
  • Damuwar MDD Kan Ci Gaba Da Rikicin Siyasa A Tsakiyar Afirka

Manzon Musaman Na MDD zuwa kasashen dake tsakiyar Afirka ya bayyana damuwar sa kan ci gaba da rikicin Siyasa a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Francois Lounceny Fall manzon musaman na MDD zuwa  kasashen yankin  tsakiyar Afirka a wannan Laraba na cewa rikicin siyasa da wasu kasashen Afirka ke fuskanta so diyawa na samo asali ne kan yadda aka gudanar da zabe a kasashen ne wanda kuma hakan ke kawo cikas a zaman lafiyar kasar.

Mista Lounceny ya ce rikicin siyasa tsakanin Gwamnati da 'yan adawa a kasar D/Congo kan zaben Shugaban kasa, da kuma aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram a kasashen yankin tabkin Tchadi, abu ne da ya sanya MDD cikin damuwa.

Har ila Wakilin MDD ya ce halin da fararen hula ke ciki a wasu kasashen Afirka musaman ma wuraren da ake rikci abu ne mai tayar da hankali sosai.