Zimbabwe : An Haramta Shigo Da Masara Daga Ketare
Gwamnatin Zimbabwe ta dau matakin haramta shigo da masara dage waje zuwa cikin kasar, bayan gamsuwa da yadda noman masara ya kasance a bana.
Ministan noma na kasar Davis Marapira ya bayyana cewa an dakatar da bada duk wani lasisi na odar masara daga ketare, da kuma hana shigo da masara daga iyakokin kasar saboda gamsuwa da yanayin noman masara na bana, wanda zai iya ciyar da al'ummar kasar gabadaya.
Bayanai daga kasar sun ce manoman kasar zasu iya samar da tonne miliyan biyu na masara a bana, wanda kuma zai iya wadatar da al'ummar kasar da yawansu ya kai miliyan 16.
Gwamnatin kasar ta ce ta ware Dalar Amurka Miliyan 200 domin sayen masara ga manoman kasar domin karkafa masu gwiwa.
Kasar Zimbabwe wacce a cen da akewa lakabi da ''rumbun alkaman Afrika'' ta fuskanci koma baya sosai a shekarun baya bayan nan saboda fari mai nasaba da canjin yanayi da ake kira El-nino daya addabi kasashen yankin kudancin Afrika.