Sabani Ya Kunno Kai A Tsakanin Kasashen Eritrea Da Djibouti Akan Iyaka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21386-sabani_ya_kunno_kai_a_tsakanin_kasashen_eritrea_da_djibouti_akan_iyaka
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabanin da ya kunno kai a tsakanin kasashen Eritrea da Djibouti ya samo asali ne daga kasabin da ke tsakanin Kasar Katar da wasu kasashen larabawa.
(last modified 2018-08-22T11:30:15+00:00 )
Jun 17, 2017 12:01 UTC
  • Sabani  Ya Kunno Kai A Tsakanin Kasashen Eritrea Da Djibouti Akan Iyaka

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabanin da ya kunno kai a tsakanin kasashen Eritrea da Djibouti ya samo asali ne daga kasabin da ke tsakanin Kasar Katar da wasu kasashen larabawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabanin da ya kunno kai a tsakanin kasashen Eritrea da Djibouti ya samo asali ne daga kasabin da ke tsakanin Kasar Katar da wasu kasashen larabawa.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephen Dujarric wanda ya ke magana akan batun ya kuma ce; Kasashen larabawan yankin tekun pasha suna fuskantar matsaloli masu yawa a gabansu da su ka kunshi tsaro da kasar Syria da Iraki da wasu wuraren, don haka suna da bukatar hada karfinsu wuri guda domin fuskantarsu.

A jiya juma'a ne dai kasar Djibouti ta zargi makwabciyarta Eretria da mamaye wani yanki da su ke takaddama akansa.

Kasar Katar dai ta janye sojojinta na tabbatar da zaman lafiya da ta girke a tsakanin kasashen biyu.