An Bukata A Tura Dakaru Na Musaman Zuwa Yankin Sahel
Ministan Harakokin wajen Kasar Mali ya bukaci Kwamitin tsaron MDD da ya tura Dakaru na musaman zuwa yankin Sahel domin yaki da ta'ddanci.
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Abdullahi Diof Ministan harakokin wajen kasar Mali na cewa kafa Rundunar hadin gwiwa na kasashen Mali, Burkina Faso, Murtaniya, Niger da Tchadi domin yaki da ta'addanci a yankin Sahel na bukatar neman izini daga Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
Kasar Faransa ta gabatarwa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kudirin tura Runduna musaman ta yaki da ta'addanci zuwa yankin Sahel , saidai Amurka ta yi watsi da wannan Kudiri.
A nasa bangare, Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Kieta kuma Shugaban ficen gadi na Rundunar hadin gwiwa na kasashen yankin Sahel biyar ya bayyana damuwar sa da adawar Amurka na tura Dakarun musaman na yaki da Ta'addanci a yankin, inda ya ce a halin da ake ciki akwai matsalar kudin da za a kafa rundunar hadin gwiwa na kasashe biyar din da su yaki ta'addanci a yankin na Sahel.