Mali : Kawancen Mayakan Jihadi A Sahel Ya Dau Alhakin Kai Harin Bamako
Kawancen Mayakan Jihadi A yankin Sahel mai alaka da kungiyar Al'Qaida ya sanar da cewa shi keda alhakin kai hari kan jami'an tsaro da fararen hula a wurin shakatawa nan na ''Le Campement Kangaba'' dake gabashin Bamako, babban birnin kasar Mali.
Kawacen da Iyad Ag Ghaly, ke jagoranta ya ce mayakan da suka ai harin 'yan kabilar fulani ne.
A yayin harin wanda aka kai ranar lahadi data gabata fararen hula hudu ne da sojin Mali guda ne suka rasa rayukansu, a yayinda kuma aka kashe ‘yan bindiga hudu wadanda suka yi yunkurin yin garkuwa da jama’a a wurin.
‘Yan bindigar sun isa ne saman babur inda suka abkawa wajen shakatawar da yawanci Turawa ke halarta a karshen mako.
Harin dai na zuwa ne mako guda bayan da kasashe hudu dake yankin na Sahel suka bukaci kasashen duniya da su agazawa yarjejeniyar hadin gwiwar kasashen biyar na G5 ta yadda za su magance matsalar tsaro a kan iyakokinsu, ciki har da batun ayyukan ta'addanci.