Italiya: An Kama Dan Najeriya Bisa Tuhumar Azabtar Da 'Yan Gudun Hijira.
(last modified Wed, 21 Jun 2017 11:55:09 GMT )
Jun 21, 2017 11:55 UTC
  • Italiya: An Kama Dan Najeriya Bisa Tuhumar Azabtar Da 'Yan Gudun Hijira.

'Yan sandan kasar Italiya sun kame wani dan Najeriya wanda ake zargi da azabtar da yan gudun hijira a kasar Libya

'Yan sandan kasar Italiya sun kame wani dan Najeriya wanda ake zargi da azabtar da yan gudun hijira a kasar Libya.

Kafar watsa labaru ta "Africa Time" ta yau laraba ta ambato 'yan sandan kasar Italiya suna cewa; Mutumin da su ka kama mai suna John Ogais, wanda ake yi wa lakabi da Rambo, ya rika azabtar da 'yan gudun hijira har sai sun kusa mutuwa.

Bugu da kari, 'yan sandan kasar ta Italiya sun sanar da samun shaida ta wasu 'yan gudun hijira akan cewa John Ogais ya taba kashe mutane biyu.

A watan da ya wuce, jami'an tsaron kasar Italiya sun kai samame a kudancin kasar inda su ka kama yan Mafia da masu hada-hadar kayan abincin da aka warewa 'yan gudun hijira.