Nijeriya : (DSS) Ta Damke Wasu Kwamandojin Boko Haram Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21612-nijeriya_(dss)_ta_damke_wasu_kwamandojin_boko_haram_biyu
Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya cewa da (DSS) ta sanar da kama wasu mutane biyu da take zargi kwamandojin kungiyar Boko Haram ne dake shirya kai hare-hare a sassan kasar da dama.
(last modified 2018-08-22T07:00:17+00:00 )
Jun 24, 2017 10:19 UTC
  • Nijeriya : (DSS) Ta Damke Wasu Kwamandojin Boko Haram Biyu

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya cewa da (DSS) ta sanar da kama wasu mutane biyu da take zargi kwamandojin kungiyar Boko Haram ne dake shirya kai hare-hare a sassan kasar da dama.

Cikin wata sanarwar da kakakin hukumar Tony Opuiyo ya fitar, ta ce an kame mutanen ne a wani a wani samame da ta kai da sanyin safiyar jiya Jumma'a.

Hukumar ta kuma yi nasara cafke kayayaki hada boma-bomai da kuma bindigogi kirar AK-47 da gurneti da kuma harsashai da butulan gas da motoci da kuma kayan lataroni da dama.

A cewar hukumar, manufarsu ita ce, shirya jerin hare-hare da ababen fashewa a garuruwa daban-daban na kasar da suka hada da Kano, Sokoto, Kaduna da Maiduguri a lokacin bukukuwan karamar sallah.

Hukumar ta kara da cewa, kungiyar ta shirya kai hare-hare wuraren taron jama'a kamar kasuwanni da wajen shakatawa da na bude ido da wajen ibadu, musammam masallatan idi da sauran wuraren dandazon jama'a yayin bukukuwan na sallah.