Jiragen Saman Yakin Masar Sun Tarwatsa Wasu Motoci A Gabashin Kasar Libiya
Jiragen saman yakin Masar sun kai hare-hare kan wasu tawagar motoci dauke da makamai da ake fasa kwabrinsu a yankin gabashin kasar Libiya kusa da kan iyaka da kasar ta Masar.
A bayanin da kakakin rundunar sojin Masar Tamir Arrafa'i ya fitar a yau Talata yana dauke da cewa: Jiragen saman yakin Masar sun yi lugudaen wuta kan wasu tawagar motoci goma sha biyu da suke dauke da muggan makamai da ake kokarin yin fasa kwabrinsu a yankin gabashin kasar Libiya kusa da kan iyaka da kasar Masar.
Bayanin ya kara da cewa: Rundunar sojin Masar ta samu bayanan sirri kan motocin da suke dauke da makaman da kuma inda suka dosa, don haka rundunar sojin kasar ta dauki matakin yin riga kafi ta hanyar tarwatsa motocin da dukkanin muggan makaman da suke dauki da su.