Tawagar ONUCI Ta Kammala Aikinta A Ivory Coast
Tawagar wanzar da zamen lafiya ta MDD cewa da ONUCI a Ivory Coast ta kammala aikinta a hukumance, bayan shafe shekaru 13 na aiki wannan kasa.
An yi bikin sauke tutar tawagar ce a jiya Alhamis tare halartar ministan cikin gida na kasar Hamed Bakayoko, da wakiliyar musamen ta sakatare na MDD a wannan kasa Aïchatou Mindaoudou da shugaban tawagar .
Mista Bagayoko, ya yi jinjina ta musamen ga tawagar akan yadda ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zamen lafiya a kasar.
A Cikin wata sanarwa da kakakin sakatare na MDD, Stephane Dujarric ya fitar, ya ce Antonio Guterres ya taya gwamnatin kasar Cote d'Ivoire murnar samun nasarar kawo karshen rikicin da ya haifar da kafa rundunar ta UNUCI.
A yau 30 ga watan Yuni ne dai wa'adin aikin rundunar ta ONUCI ke cika a hukumance.