Nijar : Za'a Canjawa 'Yan Gudun Hijira Kabalewa Sansani
Hukumomi a yankin Diffa dake kudu maso gabashin Jamhuriya Nijar, sun ce za'a canjawa 'yan gudun hijira boko haram dake rayuwa a sansanin MDD na Kabalewa wuri.
Za'a dai kaurar da 'yan gudun hijira daga sansanin na Kabalewa zuwa na Sayam wanda ya fi kasancewa cikin kasar a cewar gwamnan jihar ta Diffa Malam Laouali Mahamane.
Wannan matakin dai ya biyo bayan harin da wasu mata 'yan kunar bakin wake biyu suka kai a sansanin na Kabalewa dake kusa da iyaka da tarayya Najeriya.
Gwamnan jihar ya ce sun bukaci hukumar kula da 'yan gudun ta MDD cewa da (HCR) data hamzarta kammala aikin kwashe 'yan gudun hijira kimanin 10,000 zuwa sansanin na Sayam kafin ranar Litini.
Fararen hula biyu ne suka mutu kana wasu 11 na daban suka jikkata a harin na ranar Laraba data gabata.