Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari Yankin Kudu Maso Gabashin Niger
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyen Ngalewa da ke jihar Diffa a shiyar kudu maso gabashin Jamhuriyar Niger, inda suka kashe mutane akalla 9 tare da yin awungaba da wasu kimanin 40 na daban.
Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Maharan kungiyar ta Boko Haram sun kawo farmaki kan kauyen na Ngalewa ne da ke nisan kilomita 70 da garin Diffa a shiyar kudu maso gabashin Jamhuriyyar Niger a kan dawaki da rakuma a cikin daren ranar Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 9, sannan suka yi awungaba da wasu kimanin 40 na daban mafi yawansu mata da kananan yara.
Mayakan na kungiyar Boko Haram sun bayyana cewa: Zasu ci gaba da yin garkuwa da jama'ar da suka kama a kauyen na Ngalewa ne har sai mahukuntan Jamhuriyar Niger sun saki tarin 'yan kungiyar Boko Haram da suke tsare da su a gidajen kurkukun kasar.
Gwamnan jihar ta Diffa Dan dano Muhammad Lawwali ya tabbatar da kai harin sai dai ya ce ba su tantance yawan mutane da harin ya ritsa da su ba har sai sun kammala bincike.