Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwamnatin Somaliya
Kungiyar tarayyar Afrika ta sanar da cewa: Tana goyon bayan gwamnatin Somaliya tare da jaddada aniyarta ta karfafa matakan tsaro da zaman lafiya a kasar.
Kungiyar tarayyar Afrika a jiya Lahadi ta sanar da cewa: Tana ci gaba da jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Somaliya duk da hare-haren ta'addanci da kungiyar Al-Shabab take ci gaba da kai wa a kasar, kuma zata ci gaba da gabatar da duk wani tallafin da nufin ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da tsaro a kasar.
A nashi bangaren wakilin kungiyar tarayyar Afrika a kasar ta Somaliya Francisco Madeira ya jaddada cewa: A harin baya-bayan nan da rundunar tsaron Somaliya suka kaddamar kan mayakan kungiyar Al-Shabab sun samu nasarar kashe 18 daga cikinsu tare da jikkata wasu 19 na daban, kuma gyare-gyaren da gwamnatin Somaliya ta gudanar a fagen tsaron kasar yana ci gaba da haifar da da mai ido.